Friday, 21 June 2019

Wadannan kayatattun hotunan zasu sa ka kara son Kano

Kano ta dabo, jalla babbar Hausa, Yaro ko dame kazo an fika. Birnin Kano shine cibiyar kasuwancin Arewa inda kuma ya fi kowane gari yawan al'umma. Akwai kayan al'adu dana zamani da suka hada da kayatattun gine-gine na zamani dana tarihi masu kayatar wa.Wadannan hotunane na musamman da aka dauko wasu sassan garin Kano masu daukar hankali dan kayatarwar me karatu.

Ga wanda yasan Kano, wadannan hotunan zasu sa ta kara shiga zuciyarshi, wanda kuma be taba ziyartar Kano ba to zai so ya ziyarta.

Abin kayatarwa ga wadannan hotuna shine duk an dauke sune daga sama, ta irin jirginan mara matuki. Nuuman Ashaka ne ya dauki waau daga cikin wadannan kayatattun hotuna.

Guraren dake cikin wadannan hotuna sun hada da Ado Bayero Mall, Asibitin Malam, Aminu Kano, hotunan hawan Sallar Kano na shekarar 2019, Shoprite, Dam din Wase dake bayan Munjibir Park, gadar kofar Nasarawa da kuma kayatacciyar makarantar nan ta 'Yan dutse.

Asha kallo lafiya.
No comments:

Post a Comment