Sunday, 2 June 2019

Wata mata ta zargi Neymar da mata fyade saidai ya karyata

A jiya Asabarne rahotanni suka bayyana cewa wata mata ta zargi tauraron dan kwallon kungiyar PSG, Neymar da yi mata fyade. Matar ta bayyana cewa sun hadu a wani otalne inda Neymar din yake a buge kuma ya afka mata.A nashi martanin Neymar ya fito ta shafinshi na sada zumunta inda ya kare kanshi ya kuma karyata wancan zargi.

Neymar ya saka hotunan yanda suka ci gaba da ganawa da matar bayan haduwarsu ta farko dake nuna cewa ba fyade ya mata ba.

Neymar ya bayyana cewa, sun hadu da matar kuma suka yi abinda masoya ke yi a daki , bayannan kuma sun ci gaba da hulda wanda hakan yake nufin ba fyade ya mata ba, yace ko kadan ba da karfi ya nemeta ba.

Neymar yace ya samu tarbiyya me kyau daga gida dan haka duk wanda ya sanshi yasan ba zai aikata irin wannan gagarumin laifi da ake zarginshi da aikatawaba.

Ya kara da cewa tarko ne aka mai kuma ya fada amma wannan ya zamar mai darasi nan gaba zai kiyaye. Neymar ya kara da cewa wannan abunne yanzu ke faruwa inda ake yin irin wadannan zarge-zarge dan neman wani abu a gurin mutum

No comments:

Post a Comment