Sunday, 9 June 2019

WhatsApp na toshe masu amfani da na bogi

Kamfanin WhatsApp ya fara dakatar da masu amfani da nau'in WhatsApp da ba mallakinsa ba.


Mutane da dama ne ke amfani da wasu nau'ukan WhatsApp, da suka hada da WhatsApp Plus da GB WhatsApp da sauransu.

Kuma binciken da BBC ta gudanar ta gano cewa WhatsApp yana dakatarwa ne na wuccin gadi, har sai mutum ya sauya zuwa WhatsApp na asali kafin ci gaba da aiki da shi.

WhatsApp na cikin manyan kafofin sadarwa na tura sakwanni ta wayoyin salula da aka fi yawan amfani da su a duniya.

Kamfanin mallakin Facebook ya ce wasu ne na daban suka gina manhajojin, babu alaka tsakanin shi da su. Kuma kamfanin ya yi gargadin toshe duk wanda ya ki sauyawa zuwa asalin nasa bayan dakatar da shi na wuccin gadi.


Masana fasahar sadarwa sun ce an samar da ire-iren Whatsapp din ne domin kara wasu abubuwa da asalin WhatsApp din yake da rauni akansu.

Baban Sadiq, masanin fasahar sadarwa a Najeriya ya ce wasu masu gina manhajar salula sun bi dubaru ne na yin kari ga ayyukan Whatsapp musamman nakusu da yake da shi kan fannoni da dama.

Sai dai ya ce mutane ba su san illar amfani da wadannan manhajojin na WhatsApp da wasu suka samar ba.

"Ana amfani da su domin cutar mutane ta hanyar yi masu kutse. Idan ba mutum ya fita daga ire-irensu ba to yana cikin hatsari," in ji shi.

Ya kara da cewa saboda hatsarinsu ne ma ya sa ba a samunsu a kasuwar manhajar Google ta Play store.

Yawanci manhajoji ne da galibi ake turawa ta waya, saboda sun kasa sharudda da suka shafi hakkin mallaka da sauransu a kasuwar manhaja ta Play Store.

Bangarorin na WhatsApp na bayan fage kan ba mai amfani da su sanin lokacin da mutum ya hau WhatsApp da sauya kamannin shafinsa da tura bidiyo mai nauyi da wasu abubuwa da dama.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment