Wednesday, 26 June 2019

'Yan kwallo 3 da Ronaldo ya hure musu kunne ya hanasu komawa Real Madrid

Wasu sabbin rahotanni sun bayyana cewa tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya zamarwa tsohuwar kungiyarshi ta Real Madrid matsala wajan sayen 'yan wasa inda a yanzu haka ya hana 'yan wasa 3 komawa kungiyar.Fox Sports ta bayyana cewa 'yan wasan da Real Madrid ta nema amma Ronaldo ya hana su komawa kungiyar sune

Paul Pogba: Madrid ta so sayen Pogba kuma rahotanni sunce a shirye take ta bayar da koda miliyan 150 akan sayen nashi saboda yanda Zidane ke yunwar zuwanshi kungiyar, amma rashin son sayar dashi da Manchester United ke yi da kuma wasu rahotanni dake cewa za'a sa mai farashin da ya wuce kima da kuma jan hankalin da Ronaldo ya mai na komawa Juventus sun yi tasiri wajan kin komawar Pogba Madrid, wasu rahotannin ma sun ce ya fi son komawa Juventus da Madrid saboda Ronaldon ya ja hankalinshi.Matthijs de Ligt: Shima yana daya daga cikin wanda Real Madrid da Barcelona ke nema amma rahotanni masu karfi sosai sun bayyana cewa tuni ya zabi komawa Juventus saboda Ronaldo. A baya dai Ronaldo ya fito fili ya nemi dan wasan ya zo Juventus kuma shima De Ligt ya bayyana son buga wasa da Ronaldo .

Joao Felix: Da yawa suna bayyana wannan dan kwallon kungiyar Benfica wanda suka fito kasa daya da Ronaldo cewa shine magajin Ronaldon, shima Real Madrid ta nemeshi amma ana ganin Ronaldo ya hure mai kunne ya hanashi zuwa inda a yanzu haka wasu rahotanni ke cewa tuni har babbar abokiyar takarar Real Madrid, Atletico Madrid ta biya kudin da bata taba biya wajan sayen dan wasa ba watau militan 150 dan sayen Felix.

No comments:

Post a Comment