Pages

Wednesday 26 June 2019

'Yan Najeriya sun caccaki Ighalo saboda nunawa Ahmed Musa sonkai a wasan da suka buga da Guinea

Bayan kammala wasan da Najeriya ta buga da kasar Guinea a yau wanda aka tashi Najeriyar na cin 1-0, wasu sun hau shafukan sada zumunta inda suka rika korafi akan dan wasa Ighalo saboda wani 'sonkai' da suka zargeshi da nunawa.



A lokacin da ake buga wasan, Ighalo ya shiga gidan Guinea inda Ahmed Musa yana ta gefen shi, maimakon ya bashi kwallon sai ya buga da kanshi duk da cewa shi yana gefene amma bai samu cin kwallon ba.

Wannan yasa da dama suka hau shafin Twitter inda suka bayyana takaicinsu akan wannan bari da Ighalo yayi, wasu sun ce da ya ba musa watakila da ya ci kwallon,wasu kuwa cewa suka yi Ighalon yayi sa'a Najeriya ta yi nasara a wasan da ya sha mummunan raddi.



Ga martanin da wasu suka yi akan wannan lamari kamar haka:







No comments:

Post a Comment