Sunday, 16 June 2019

Yanda aka daura auren Ramos da matarshi data bashi tazarar shekaru 8

An daura auren tauraron dan kwallon Real Madrid, Sergio Ramos da masoyiyarshi, Pilar Rubio wadda shahararriyar me gabatar da shirye-shirye ce a gidan talabijin din kasar Sifaniya.Auren nasu da aka daura jiya Asabar, ya samu halartar manyan baki, 'yan uwa da abokan arziki da suka hada da shahararrun taurarin kwallon kafa irin su, David Beckham, Jordi Alba, Luka Modric, Keylor Navas, Roberto Carlos, Alvaro Morata dadai sauransu.

Mahaifiyar Ramos ce ta gabatar dashi a wajan bikin inda suka fito makale da hannun juna.

Wani abu da ya dauki hankula dangane da auren shine, Matar ta Ramos ta girmeshi da yawan shekaru 8 yayin da shi yake da shekaru 33 ita kuwa tana da shekaru 41 ne.

An daura aurenne a birnin Seville na kasar Sifaniya inda jama'a da dama suka hadu dan shaidawa.

Masoyan sun kasance tsawon shekaru 7 tare inda suka samu 'ya'ya 3.

An hau motocin alfarma sosai a wajan sannan Ramos ya bayyana farin cikinshi da samun dace da masoyiya ta kwarai.

No comments:

Post a Comment