Saturday, 15 June 2019

'Yansandan Brazil sun maka matar dake zargin Neymar da yi mata fyade a Kotu bisa zargin bata suna

'Yansandan kasar Brazil sun bayyana cewa sun shigar da karar matarnan da ke zargin tauraron dan kwallon kafa, Neymar da yi mata fyade bisa zargin bata musu suna da ta yi.A wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin din SBT, matar ta bayyana cewa, an saye 'yansandan.

A ranar Alhamis, 'yansandan sun fitar da sanarwa inda suka bayyana cewa basu goyon bayan kowane bangare akan lamarin.

A ranar Talata ne dai lauya na 3 ya janye daga wakiltar Najila Trindade inda yace bashi ba ta.

Hakanan matar ta bayyana cewa tan da wani bidiyo dake tabbatar da cewa Neymar ya ci zarafinta.


No comments:

Post a Comment