Wednesday, 12 June 2019

Za mu iya raba mutum miliyan 100 da talauci>> Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta iya fitar da mutum miliyan 100 daga talauci idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata.


"Akwai alaka tsakanin talauci da koma bayan tattalin arziki da cin hanci da kuma rashin zaman lafiya," a cewar shugaban, wanda ke magana a ranar bikin cika shekara 20 da kawo karshen mulkin soji a kasar.


Sai dai bai yi wani cikakken bayani kan yadda gwamnati za ta yi hakan ba, abin da ya sa wasu ke ganin kalamai ne kawai irin na 'yan siyasa da sukan yi domin birge jama'a ko jan hankalin masu sauraransu.

Najeriya ta fi kowacce kasa yawan arzikin man fetur da kuma jama'a a Afirka, amma tana sahun gaba-gaba a jerin kasashen da ke fama da rashin ci gaba, abin da ake alakantawa da cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci.

Wannan ne karon farko da ake yin bikin Ranar Demokuradiyyar a 12 ga watan Yuni.

An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma "rage radadin" alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993.

Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojin lokacin ta soke.

Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la'akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan.

No comments:

Post a Comment