Monday, 8 July 2019

A karin farko Eden Hazard ya fara Atisaye a Real Madrid: Saidai an lura da wani abin damuwa da ya sameshi

Tsohon tauraron dan kwallon Chelsea wanda ya koma bugawa Real Madrid wasa, Eden Hazard kenan a wadannan hotunan da a karin farko zai fara atisaye a sabuwar kungiyar tashi.Saidai da dama, musamman magoya bayan Chelsea din su lura da wani abu na cewa Hazard din yayi kiba.

Kibar tashi ba mamaki bace ganin cewa daga hutu ya dawo amma abin jira a gani shine ko kwalliya zata biya kudin sabulu?


No comments:

Post a Comment