Tuesday, 9 July 2019

AFCON: Yanda za'a buga wasannin Quarter Final: Za'a yi amfani da VAR: Da wanda suka fi yawan kwallaye a gasar

Bayan kammala wasannin kasashe 16 da suka rage a gasar neman cin kofin nahiyar Afrika dake gudana a kasar Egypt, a yanzu an fitar da yanda za'a buga wasannin kusa dana kusa dana karshe a gasar.A gobe, Larabane za'a fara wasannin kamar haka:

17:00 Senegal vs Benin
20:00 Nigeria vs South Africa

Sai kuma wasannin Ranar Alhamis da za'a buga kamar haka:
17:00 Ivory Coast vs Algeria
20:00 Madagascar vs Tunisia

Wani ci gaba da aka samu a gasar shine a wadannan wasanni na kusa dana kusa dana karshe za'a yi amfani da na'urar nan ta taimakawa alkalin wasa wajan yanke hukunci, watau VAR dake yawan jawo cece-kuce a wasanni.

Daya daga cikin wakilan hukumar shirya wasannin nahiyar Afrika, Souleyman Waberi ya shaidawa manema labarai cewa, an shirya tsaf dan fara amfani da na'urar domin tuni har an yi amfanin gwaji da ita.

Kamin a fara wadannan wasanni na gobe ga 'yan wasan da suka fi cin kwallaye da yawa a gasar kamar haka:

'Yan kwallo 4 ne suka ci kwallaye 3, sune Ighalo na Najeriya, Sai Sadio Mane na kasar Senegal, Cedric Bakambu na kasar DR Congo, sai Adam Ounas na kasar Algeria. Saidai an fitar da DR Congo daga gasar, saboda haka Bakambu baya cikin wanda zasu lashe kyautar takalmin zinare.

'Yan kwallon da suka ci kwallaye 2 a gasar sune, Belaili, Mahrez wanda duk 'yan kasar Algeria ne sai kuma Elmohamady, Salah 'yan kasar Egypt, sai J. Ayew na kasar Ghana, da Bahoken dan kasar Kamaru, da En-Nesyri dan kasar Morocco, sai Okwi dan kasar Uganda, da Olunga dan kasar Kenya, sai Pote dan kasar Benin da Yattara dan kasar Guinea, sai kuma Zaha dan kasar Ivory Coast.

No comments:

Post a Comment