Thursday, 11 July 2019

AFCON:Labarin Wasanni: Najeriya zata hadu da Algeria a wasan kusa dana karshe

Labarin wasanni na yammacin nan ya bayyana cewa kasar Algeria da Kwadebuwa da suka buga wasan kusa dana kusa dana karshe a yau sun tashi kunnen doki 1-1 inda saida suka buga wasa na tsawon mintuna 120 amma babu wanda yayi nasara a wasan dalilin haka aka je bugun daga kai sai gola.Labarin wasanni ya ci gaba da cewa, an tashi wasan Algeriya nada nasara akan kwadebuwa da ci 4-3 a bugun daga kai sai gola da suka yi.

Wannan na nufin Algeriar ta kai wasan kusa dana karshe kuma zata hadu da Najeriya a ranar Lahadi me zuwa in Allah ya kaimu.

No comments:

Post a Comment