Wednesday, 10 July 2019

AFCON:Labarin Wasanni:Najeriya ta kai wasan kusa dana karshe bayan cin Afrika ta kudu 2-1:Shugaba Buhari da Atiku sun tayasu murna

Labarin wasanni da dumi-duminsu cikin darennan na cewa Super Eagles na Najeriya sun lallasa Bafana-Bafana na kasar Afrika ta kudu da ci 2-1 a wasan kusa dana kusa dana karshe da suka buga yau na neman daukar kofin Nahiyar Afrika dake gudana a Kasar Egypt.Chukwueze ne ya fara ciwa Najeriya kwallo ana mintuna 27 da wasa amma hankalin 'yan Najeriya ya tashi yayin da kasar Afrika ta kudu ta rama kwallon ta hannun Zungu yayin da ake mintuna 71 da wasa. Saura minti 1 tal a tashi, dan wasan Najeriya, Troost-Ekong ya ciwa Najeriya kwallo ta biyu wanda a haka aka tashi wasan.

Wannan nasara dai na nufin Najeriya ta kai wasan kusa dana karshe kenan a gasar.

Chukwuezene aka baiwa gwarzon wasan saboda bajintar da ya nuna.

Hakanan,Labarin wasanni na hutudole.com ya ci karo da wani hoto da ya dauki hankula sosai wanda ya nuna 'yan kasar Egypt suna wa Bafana-Bafana baibai. Idan dai ba'a mantaba a labarin wasanni na baya munji yanda jaridar Vanguard ta ruwaito wasu daga cikin 'yan kasar ta Egypt suna rokon 'yan Najeriya da su rama musu cin da Kasar Afrika ta kudu ta musu, yaudai kam zasu kwana cikin farin ciki dan kasar data fitar dasu itama an fitar da ita.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari tuni ya taya Super Eagles murnar wannan nasara inda yace sun cancanci samunta, da yake magana ta hannun hadiminshi, Malam Garba Shehu, Shugaban yace 'yan Najeriya zasu ci gaba da yi musu addu'a da fatan Allah ya basu nasara a sauran wasanni biyun da suka rage dan daukar kofin.

Labarin wasanni na hutudole.com ya kuma ci karo da sakon taya murna na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar shima yana taya Super Eagles murnar wannan nasara inda yace kiris ya rage a kafa tarihi kuma yana alfahari dasu.

Karshen labarin wasannin kenan a wannan lokaci.

No comments:

Post a Comment