Friday, 12 July 2019

Amaryar Da Ake Shirin Aurenta, Fateema Abubakar Isma’il Ta Rasu

INNA LILLIAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN
Fateema ‘yar Engineer Abubakar Isma’il da Zuwaira Ahmad wacce ta kammala jami’ar Bayero a bana ta rasu ne a ranar Talatar da ta gabata, bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya ta kwana biyu. Ta rasu ne ragowar kwanaki kalilan a yi bikin aurenta.


Wannan mutuwa ta girgiza kowa. Fateema mutuniyar kirki ce, ba ta duba girman gidansu sai na al’umma, an kammala komai na shirin biki sai ciwon sikilarta ya motsa bayan an kaita asibiti an kwantar da ita, Allah ya nuna mata cewa ciwon ba na tashi ba ne, inda ta dinga yi wa mahaifiyarta da kakarta sallama tana cewa 'ita fa tafiya za ta yi’ a washe gari kuwa ta cika.

Allah ya karbi bakuncin Fatima, ya gafarta mata, ya kuma baiwa iyayents hakurin jure rashin.
Sa'adatu Ahmad.


No comments:

Post a Comment