Wednesday, 10 July 2019

An caccaki Hadimin Buhari saboda murnar fasa zuwan Nicki Minaj Saudiyya da yayi

Bashir Ahmad me taimakawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari akan sabbin kafafen sadarwa yayi murnar fashin zuwa kasar Saudiyya da mawakiyar kasar Amurka, Nicki Minaj a yi. Inda ya rubuta a shafinshi cewa, Arewa Twitter ta yi nasara. Wannan abu ya jawo wasu, musamman daga kudancin Najeriya suka rika caccakar bashir.


Wani ya gayawa Bashir din cewa ga matsalolin tsaro da matsalar aikin yi da almajiranci ba zaka rika yin magana akan su ba sai wannan?

Wani kuma ya bayyana bashir a matsayin abin kunya ga matasa inda yace abin takaicine yanda ya samu kanshi a matsayin da za'a rika jinshi.

Saidai bashir din ya sake mayar musu da martani inda yace yana nan akan bakanshi na cewa Arewa Twitter ta yi nasara, su yi abinda zasu yi.No comments:

Post a Comment