Saturday, 13 July 2019

An sake dakile yunkurin juyin mulki a Sudan

Gwamnatin Wucin gadi ta Sudan ta sanar da dakile wani sabon yunkurin na yin juyin mulki, kuma ta kama wanda ya jagoranci yunkurin.


Shugaban Kwamitin Tsaro na Gwamnatin Janaral Jamal Umar ya shaida wa tashar talabijin ta kasa ta Sudan cewa wasu jami'an soji da suka yi ritaya da masu ci daga rundunar sojin da hukumar leken asiri sun yi yunkurin kifar da gwamnatinsu kuma an kama kwamandan da ya jagoranci yunkurin tare da sauran jami'a 23.

Janaral Umar ya kara da cewa wannan yunkuri na juyin mulki na da manufar lalata yarjejeniyar da aka yi da Dakarun Hadin Kan Neman 'Yanci da Kawo Sauyi a Sudan.

Kakakin gwamnatin Wucin Gadi ta Sojin Shamsuddin Kabbashi kuma ya fadi cewa a watan Yunin da ya gabata ma an yi kokarin yin juyin mulki a Sudan.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment