Friday, 12 July 2019

A hukumance: Barcelona ta bayyana sayen Antoine Griezmann daga Atletico Madrid

Barcelona ta sayi dan wasan gaban Faransa Antoine Griezmann daga Atletico Madrid.


Kungiyar ta sayi dan kwallon ne a kan Yuro miliyan 120 - wato kimanin fam miliyan 107 ke nan.

Dan wasan mai shekara 28 wanda ya lashe kofin duniya ya kulla yarjejeniyar shekara biyar ciki har da kudin da idan wata kungiyar za ta dauke idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba za ta biya wato Yuro miliyan 800.


Griezmann ya koma Atletico ne daga Real Sociedad a shekarar 2014 kuma ya ci kwallaye 133 a wasa 256 da ya buga wa kungiyar.

Ya sabunta yarjejeniyarsa ta shekara biyar a watan Yunin shekarar 2018 ne, amma a watan Mayu ya ba da sanarwar barin kungiyar a kakar bana.

Dan wasan ya zama shi ne dan wasa na shida da ya fi tsada da Barcelona ta saya a bayan Neymar, Kylian Mbappe, Philippe Coutinho, Joao Felix da kuma Ousmane Dembele.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment