Monday, 1 July 2019

Atiku da PDP zasu gabatarwa da kotu shaidu 400 dan kalubalantar zaben Buhari

Jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta,Atiku Abubakar ta bayyanawa kotun sauraren karar zabe cewa tana da shaidu 400 da zata gabatar a kalubalantar nasarar zaben da shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya lashe.Alkalan kotun da me shari'a, Muhammad Garba ke jagoranta sun bayyanawa Atiku cewa yana da kwanaki 14 domin gabatar da wadannan shaidu nashi.

Lauyan Atikun, Dr. Livy Uzoukwu ya bayyana cewa zasu yi iya kokarinsu wajan gabatar da shaidun da suka sawwaka a wannan kwanaki da aka basu.

No comments:

Post a Comment