Wednesday, 10 July 2019

Atiku Ne Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Jihar Katsina>>Shugaban jam'iyyar PDP a Katsina

Shugaban Jam'iyyar PDP na Jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya yi da'awar cewa jam'iyyarsa ce ta yi nasarar lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar 23 February, 2019 a jihar ta Katsina, inda dan takarar jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben da tazara dubu talatin da ukku 33,000, a zaben da Hukumarr Zabe ta kasa Mai Zaman Kanta INEC ta ayyana jam'iyyar APC ta samu Nasara.


Majigiri ya bayyana haka ne a lokaci da yake bada sheda a gaban kotun dake sauraran korafin zabe shugaban kasa a Abuja a jiya Talata. Inda ya ce sakamakon Zaben da jam'iyyarsa ta PDP ta tattara a Jihar Katsina ta hanyar wakilan jam'iyyarsa  su dubu hudu da dari Tara da biyu (4902) ya nuna cewa APC ta samu kuri'u 872,000. Ita kuwa jamiyyar PDP ta samu zunzurutun kuri'u 905,000.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri shi ne shaida na takwas da jamiyyar PDP ta gabatar a gaban kotun da mai Shari'a Muhammed Garba yake jagoranta, da alkalai biyar, kan karar da jamiyyar PDP ke kalubalantar nasarar shugaban Kasa Muhammadu Buhari Da jam'iyyar APC A Zaben 2019.

Shugaban jamiyyar PDP na jihar Katsina ya Kara da cewa "jamiyyar mu ta PDP ce muka samu nasara. Domin APC ta samu Kuri'u 872,000, mu kuma jamiyyar PDP mun samu Kuri'u 905,000. Wannan sakamakon zaben da muka tattara, ta hanyar wakilanmu da ke kowacce rumfa, ba wanda ke rumbun tattara bayanai ba ko Wanda Hukumar ta ayyana ba.


No comments:

Post a Comment