Thursday, 11 July 2019

Bayan sayen fom din sake tsayawa takarar gwamna, gwamna Yahaya Bello ya je gun shugaba Buhari neman Tabarruki


Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kenan a wadannan hotunan tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin tarayya inda gwamnan ya kaiwa shugaban fom din sake tsayawa takarar gwamna a karo na biyu da ya siya jiya laraba.

Gwamna Yahaya Bello ya kasance na gaba-gaba wajan nuna goyon bayanshi ga shugaba Buhari kuma ga dukkan alamu shima zai so shugaban ya bashi goyon baya dan ganin ya sake darewa a kujerar ta gwamnan jihar Kogi.

Saidai Gwamna Yahaya Bello na fuskantar tirjiya daga wasu 'yan jam'iyyar APC na jihar Kogin inda suka ce ba zasu yi shi ba.

No comments:

Post a Comment