Friday, 12 July 2019

Cin hanci yawa 'Yansanda, Majalisar tarayya da bangaren shari'a katutu a Najeriya>>Bincike

Kungiyar dake saka ido akan harkar rashawa da cin hanci ta Duniya, TI ta fitar da sakamako wani bincike da ta yi a kan cin hanci da rashawa na Duniya yankin Afrika inda tace cin hanci a Afrika yana hana ci gaban siyasa, tattalin arziki da kuma ci gaban al'umma.Labarai sun bayyana cewa sakamakon da kungiyar ta fitar jiya, Alhamis ya nuna cewa a Najeriya, 'yansanda sune na daya a wajan cin hanci da rasha sai kuma majalisar tarayya dake take musu baya sai kuma bangaren gwamnatocin kananan hukumomi da yazo na 3.

Na hudu a cin hanci a Najeriya sune bangaren shari'a, sai bangaren kasuwanci da kuma fadar shugaban kasa, masu biye wa wadannan sune kungiyoyi masu zaman kansu da shuwagabannin gargajiya da kuma bangaren addini.

Saidai majalisar tarayya ta hannun shugaban kwamitin hulda da jama'a na majalisar dattijai,Adedayo Adeyeye yace wannan bincike an yi shine bisa kintace kawai dan ba'a yi bincike na asali ba kuma majalisar tasu a wannan akrin zata canja tunanin mutane akan majalisa.

No comments:

Post a Comment