Tuesday, 9 July 2019

Da dan kudu ne ya samu damar Dangote da yafi kowa kudi a Duniya>>Inji Tsohon ministan Jonathan

Tsohon ministan harkokin jiragen sama a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan watau Femi Fani Kayode, ya bayyana cewa da ace dan kudu ne yake samun irin damar da me kudi na daya a cikin bakaken fatar Duniya wanda kuma dan Arewane, watau Aliko Dangote to da sai ya zama wanda ya fi kowa kudi a Duniya.

Kayode da yake mayar da martani ga El-Rufai akan maganar cewa Har yanzu Dangotene wanda yafi kowane dan kasuwa kudi a Nigeria kuma ba dan kudu bane, mungodewa Allah da wannan yace:

Da ace wani dan kasuwa daga kudu zai samu itin tallafin da Dangote ya rika samu daga gwamnatin tarayya tsawon shekaru 40 to da yanzu ya zama wanda yafi kowa kudi a Duniya.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce.No comments:

Post a Comment