Saturday, 6 July 2019

Da gangan aka bani jan kati: Kuma da gangan aka hana mu zuwa wasan karshe aka baiwa Brazil dama>>Messi

Bayan kammala wasan neman matsayi na uku da aka yi tsakanin kasar Argentina da Chile wanda ya kare ba dadi, An baiwa Messi da Medel jan kati sannan Argentinar ta yi nasara da ci 2-1. Messin ya ki zuwa karbar kyautar da ake baiwa 'yan wasa inda yace ba zai je a yi cin hanci dashi ba.Bayan kammala wasan Messi ya ki zuwa inda ake rabawa 'yan wasa kayan karramawa inda da yake hira da 'yan Jarida aka tambayeshi dalili sai ya bayyana cewa, Ba zai je ya taimakawa cin hanci ba.

Messi ya zargi cewa akwai cin hanci a tsakanin masu shirya wasan.

Sannan yayi zargin cewa jan katin da aka bashi dama can tsararren abune da aka shirya mai saboda kalaman da yayi bayan kammala wasansu da Brazil inda yace an nuna son kai.

Sannan ya kara da cewa ko zuwan Brazil wasan karshe shima shirine, Argentina suna da kyau kuma sun cancanci zuwa wasan na karshe amma aka hanasu aka baiwa Brazil damar zuwa.

Messi yace yana son fadin gaskiya dan yana jin dadi idan yayi hakan.

No comments:

Post a Comment