Saturday, 13 July 2019

Daidai da rana daya ban taba yin dana sanin kawo shari'ar musulunci jihar Zamfaraba>>Tsohon gwamnan Zamfara, Yarima


Yerima Zamfara governor
Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Sani Yariman Bakura ya bayyana cewa gwamnan Zamfara na Yanzu Bello Matawalle yasan cewa ba talakawane suka zabeshi ba, hukuncin kotu ne da ikon Allah ya kawoshi kam mulki.

Yarima ya bayyana hakane ga 'yan jarida a ganawar da yayi dasu a Abuja babban birnin tarayya, ya kuma kara da cewa idan gwamnan naso ya kara hawa kan kujerar gwamnan a karo na biyu to yasan abinda zai yi a matsayinshi na dan siyasa.

Yarima ya karyata rade-radin dake yawo akan cewa wai shi da shugaban APC, Adams Oshiomhole sun yi alkawari da gwamnan akan cewa yaje ya nemi hakkinshi a kotu, idan ya zama gwamna daga baya sai ya dawo APC, yace wannan ba gaskiya bane, yace yayi aiki da Matawalle a matsayin kwamishina na shekaru 8 sannan yayi dan majalisa to wannan ya ishehi mutane su san ko shi waye.

Yarima kuma ya kara da cewa daidai da rana daya bai taba yin dana sanin kawo shari'ar musulunci jihar Zamfara ba, yace akwai maganar neman kafa shari'ar musulunci tun ma kamin ya kawo ta jihar Zamfara a Najeriya.

Sannan yace kawo shari'ar ya taimaka a jihohi da dama na Arewacin kasarnan, kawai abinda mutane sukewa kallon shari'ar shine hukuncin cire hannu da sauransu maimakon su kalli cewa misali yanzu a jihar Zamfara babu inda zaka samu gidan karuwai koda guda daya.

Da yake magana akan 'yan shi'a,Yarima yace babu wanda ya agari gwamnati kuma idan sun zama matsala ga harkar tsaro to gwamnatin tasan abinda ya kamata ta yi akai.

No comments:

Post a Comment