Saturday, 13 July 2019

Dan uwan Zidane ya rasu: Ya bar Madrid zuwa Faransa


Me horas da 'yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane yayi rashin dan uwanshi me suna Farid. Real Marid dince ta tabbatar da haka a wata gajeruwar sanarwa data fitar inda Zidane din ya tafi Faransa gurin iyalinshi jiya Juma'a.

A yayin fara Atisaye na rana ta hudu, bayan dawowa daga hutu da 'yan wasan na Real Madrid ke yi, sun yi shiru na minti daya dan nuna alhini ga rashin dan uwan na Zidane.

David Bettoni, mataimakin Zidane din ne ya amshi ragamar horas da 'yan wasan kamin ya dawo. 

No comments:

Post a Comment