Thursday, 11 July 2019

Dangote da Otedola sun yi alkawarin siyan duk kwallon da Super Eagles zasu nan gaba kan sama da naira miliyan 26

Manyan attajiran masu kudin Najeriya biyu, Aliko Dangote da Femi Otedola sun yi alkawarin baiwa kungiyar kwallon Najeriya, Super Eagles Dala dubu 75 akan kowace kwallo da zasu ci nan gaba.Wannan kudi kwatankwacin sama da Naira miliyan 26 kenan.

Dangote yayi alkawarin bayar da Dala dubu 50 akan kowace kwallo yayin da Otedola yayi alkawarin bayar da dala dubu 25 akan kowace kwallo da Najeriya zata ci nan gaba.

Kamfanin Aiteo a baya ya baiwa kungiyar ta Super Eagles kyautar dala dubu 75 saboda nasarar da suka samu akan kasar kamaru da ci 3-2.

Sannan wani dan kasuwa me suna Wells Okunbo yayi alkawari baiwa kowane da wasan kungiyar dala dubu 20 kuma gwamnan Legas, Babajide Sonwo Oluwo shima ya baiwa 'yan wasan dala dubi 5 kowanensu.


No comments:

Post a Comment