Wednesday, 10 July 2019

Gidan cin abincin Messi na rabar da abinci kyauta ga mabukata

A kasar tauraron dan kwallon Barcelona, Lionel Messi ta haihuwa, Argentina akwai mutane da dama dake cikin halin rashin muhalli da kuma rashin abinci. Wannan yasa kungiyoyin agaji na Duniya daban-daban kai dauki kasar, shima Mesin ba'a barshi a bayaba wajan baiwa 'yan kasar nashi irin tashi gudummuwar.A cikin labarin wasannin data ruwaito, Marca ta bayyana cewa, gurin cin abincin na Messi tun ranar Juma'ar data gabata yake ta baiwa mabukata a kasar abinci da abubuwan sha kyauta.

Wani dake aiki a gurin ya bayyanawa Marca cewa suna bayar da abincin da abinsha ga mabukata dake ta turuwa a gurin kuma zasu ci gaba da hakan har zuwa kwanaki 15.

No comments:

Post a Comment