Tuesday, 9 July 2019

Girgizar kasa ta afku a Iran

Girgizar kasa mai karfin awo 5.7 ta afku a garin Madjidu Sulaiman dake jihar Huzirta ta kasar Iran.


Cibiyar Kula da Motsawar Kasa ta Jami'ar tehran ta bayyana cewa girgizar ta afku da misalin karfe 11.30 na ranar Litinin din nan.

Girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 17.

Ba a bayar da wata sanarwa ba game da ko girgizar ta janyo wata asara ba.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment