Wednesday, 10 July 2019

Hadimin Shugaban Kasa, Bashir Ahmad Na Dab Da Angoncewa

Ni, Bashir Abdullahi El-bash, ina mai farin cikin sanar da ilahirin masoya malam Bashir Ahmad, babban hadimi na musamman ga Shugaban kasar Nageria, Malam Muhammadu Buhari kan kafafen sadarwa na zamani (New Media) da su kasance cikin shirin halartar gagarumin shagalin bikinsa.


Dama can ya kamata tuntuni ace mutum mai matsayi irin Bashir ya yi aure, amma Allah bai kawo lokacin ba sai yanzu.

Dan haka dai jama'a yanzu lokaci ya yi, ba kusa ba nesa nan gaba kadan daga yanzu zuwa kowane lokaci za a fitar da sanarwar ranar da Mallam Bashir zai angwance tare da amaryarsa.

Kowa ya shirya  ya zauna cikin shirin zuwa Birnin Dabo halartar wannan gagarumin biki na ɗan'uwa Bashir Ahmad, babban mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari a kafafen sadarwa na zamani (New Media).

Mu kuma da mu ke zaune babu ma budurwar, mu na fatan Allah ya kawo mana lokacin cikin koshin lafiya.
Rariya.


No comments:

Post a Comment