Thursday, 11 July 2019

Hotunan 'yanda 'yansanda suka kama 'yan shi'a masu zanga-zanga a Abuja

Labarai a yau sun bayyana yanda 'yan Shi'a suka sake fitowa kan titin babban birnin tarayya,Abuja suna zanga-zangar neman gwamnatin tarayya ta saki shugabansu, Shiekh Ibrahim Zakzaky. A yauma an samu dambarwa tsakanin 'yan shi'ar da jami'an tsaro.Labarai sun bayyana yanda 'yansandan suka harba barkonon tsohuwa da kuma harbi a iska dan tarwatsa zanga-zangar sannan kuma sun kama wasu daga cikin 'yan shi'ar.

Wadannan hotunan sun nuna yanda ake dora 'yan shi'ar da aka kama a motar jami'an tsaro.No comments:

Post a Comment