Friday, 12 July 2019

Ina cikin matsi kan fitar da sunayen ministoci amma mutanen dana sani kadai zan nada>>Shugaba Buhari

Labarai na yau na nuni da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana akan fitar da sunayen ministocinshi inda ya bayyana cewa an matsamai akan ganin ya fitar da sunayen amma ba zai yadda wani ya takuramai yayi hakan ba.Shugaban yayi wannan maganane a daren jiya, Alhamis yayin liyafar cin abincin dare da ya shiryawa shuwagabannin majalisar tarayya a fadarshi dake Abuja,kamar yanda labarai daga sanarwar me magana da yawunshi, Femi Adesina ya fitar.

Da yake magana a wajan taron, shugaban yace,na san da yawanku nan kuna so kuga sunayen ministoci saboda ku tafi hutu hankulanku kwance, ina cikin matsi akan fitar da sunayen ministocin amma bazan yadda wannan yasa in yi gaggawar yin hakan ba.

Labarai sun ci gaba hakamar haka, A mulkinana baya yawancin ministocin dana yi aiki dasu bansansu ba, na nadasune bisa shawarar jam'iyya da kuma wasu mutane da suka kawo minsu amma a wanan karin hakan ba zata faru ba, zan nada mutanen dana sanine kawai a matsayin ministoci, inji shugaban.

Idan dai ba'a mantaba,a kwanakin baya, labarai sun bayyana yanda uwargidan shugaban kasar, A'isha Buhari ta taba fitowa ta yi zargin cewa shugaban baisan da yawa daga cikin ministocinshiba, asalima ba wada suka taimakamai wajan zama shugaban kasa bane.

A wajan liyafar cin abincin ta daren jiya, shugaban Buhari ya kuma yaba da yanda aka gudanar da zaben shuwagabanjin majalisun tarayyar cikin kwanciyar hankali.

Hakanan shima kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa maganar da akace yayi a baya ta cewa wai Buhari zai kai musu sunayen ministoci cikin wannan satin ba gaskiya bane, kamar yanda labarai daga jaridar Punch suka bayyana.

Abinda nace shine watakila shugaban ya kawo mana sunayen ministocin bawai tabbatarwa na yi ba, Injishi.

No comments:

Post a Comment