Thursday, 18 July 2019

JARUMIN 'DAN SANDA DA YA YAKI BOKO HARAM DA RUHINSA YA ZAMA ABIN WULAKATANTAWA

Jama'a wannan da kuke gani a hoto jarumin 'dan sanda ne, sunansa CSP Dauda Buba Fika, shine kwamandan rundinar 'yan sanda masu kwantar da tarzoma (MOPOL) rundina ta 41 dake da sansani a garin Damaturu jihar Borno.


CSP Dauda Buba Fika jarumin 'dan sanda ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa a tarihin yaki da kungiyar annoba 'yan ta'addan Boko Haram, kishin jiharsa da yankinsa ya sa ya koma gida domin kawo karshen ta'addancin Boko Haram.

A shekarar 2016 shi ya jagoranci rundina ta musamman suka 'yanto garinsa Fika daga hannun Boko Haram.

Ya taba jagorantar wata hadaddiyar rundinar jami'an tsaro suka je suka kubutar da 'yan sanda 18 daga hannun Boko Haram, 'yan ta'addan Boko Haram sun masa harin kwanton bauna sau 4 yana tsallakewa da kariyan Allah.

A tarihin yaki da Boko Haram cikin 'yan sanda babu wanda ya nuna jarumta fiye da shi.
Amma karshen al'amarinsa wasu gurbatattun sojojin Nigeria da suke aiki a jihar Yobe sun harbe shi da bindiga a ranar 13-4-2017 amma bai mutu ba.

Kamar yadda yake fadawa wakilin jaridar Premium Times daga gadon asibiti inda yake jinya  yanzu haka a Kasar London, CSP Dauda Buba Fika yace watarana yana tafiya tare da yaranshi a cikin birnin Damaturu jihar Yobe, sai yaranshi suka samu sabani da wasu sojoji akan hanyar wucewa.

Yace bayan ya isa gida, bai jima da isa ba sai ga wasu sojoji sukazo gidansa sukaci zarafinsa, sannan suka daukeshi suka tafi dashi sansaninsu suka jefa shi a cikin wani rami, har sun dana bindiga zasu harbeshi a lokacin sai babban su ya hana, ya sa aka fito dashi daga ramin.

A lokacin da yaransa suka samu labari sojoji sun kamashi, shine suma suka dauki bindigogi suka tafi sansanin sojojin domin su kubutar da Maigidansu suna ta harbi a sama, CSP Dauda yace sai ogan sojojin ya kaini ofishinsa bayan sun fito dani daga rami, yace na je na rarrashi yarana su dena harbi.

Bayan na fito na tarar da yarana, sai na kwantar musu da hankali, sai suka duba ni don su tabbatar ba'aci zarafina ba, nace kada su damu, su koma sansaninsu, sai suka bi umarni na, sai ya rage da ga ni sai yarana 'yan sanda Mopol guda biyu, to a lokacin ne ba mu sani ba ashe akwai wasu sojoji suna bin diddigin mu, kawai sai suka bude mana wuta, sun samu nasaran hallaka yarana Mopol guda biyu da nake tare da su a lokacin, ni kuma harsashin bindiga guda biyu ya taba ni a cinya.

CSP Daudu Buba Fika yace yana kwance cikin jini sai wani babban soja yazo gurin, yace a dauke ni a kaini asibitin sojoji, a lokacin ne Kwamishinan 'yan sanda na jihar Yobe ya samu labarin abinda ya faru dani, kuma yazo don ya bincika ko ina raye, daga nan asibitin sojoji sai ya bada umarni a kai ni Abuja don na samu nagartaccen jinya, to a lokacin an rufe filin tashi da saukan jiragen sama na Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja saboda ana gyara, sai aka kaini Kaduna, washe gari aka wuce dani Abuja a motar asibiti.

Labarin yana da tsayi, amma har yanzu wannan bawan Allah yana kwance a asibiti a birnin London, kuma ya makance sakamakon tiyatar kwakwalwa da aka masa a Abuja bisa gangancin likita, kuma yace yayi mamaki da rundinar sojin Nigeria tayi watsi dashi, yace yana da yakini muddin shugaban sojojin Nigeria janar Buratai ya samu labarin halin da yake ciki da zai taimaka masa.

Ya sayar da gidansa, da kadarorinsa akan neman lafiya, yayi godiya ga rundinar 'yan sandan Nigeria da take taimaka masa wajen biyan kudin aikin jinya da ake masa a London.

Rayuwa kenan, mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu domin a kawo karshen rikicin Boko Haram wannan shine irin abinda ake saka musu da shi a Kasar, Allah Ka jikan Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, jarumin soja, babban direban tankar yaki, sai da ya gama cin Boko Haram da yaki kawai akace wai wasu tsirarun 'yan Boko Haram sun kashe shi, ance za'ayi bincike saboda kisan yana da sarkakiya, amma binciken ya bi iska, wannan itace kasarmu Nijeriya.

Muna rokon Allah Ya bawa CSP Dauda Fika ingantaccen


Datti Assalafy.

No comments:

Post a Comment