Tuesday, 2 July 2019

Juventus ta kara dauko sabon dan wasa

Zakarun Italiya Juventus sun kammala daukar dan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot daga Paris St-Germain.


A karshen watan Juni ne kwantiragin dan kwallon mai shekara 24 ta kare a PSG, a don haka ya tafi a kyauta ba tare da an biya kudi ba.

Tun a watan Disamba kocin PSG Thomas Tuchel ya daina sanya dan kwallon a wasa bayan da ta bayyana cewa ba ya so ya tsawaita zamansa a kulob din.

A bara ne Rabiot ya ki yarda a sanya shi a jerin sunayen 'yan wasa masu jiran tsammani a tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya bayan da ba a sanya shi cikin tawagar kai tsaye ba.

Juventus ta wallafa hotunan dan wasan a ranar Lahadi a shafin Twitter lokacin da ya isa birnin Turin a jirgin sama domin a gwada lafiyarsa.

Shi ne dan wasa na biyu da Juventus ta dauka ba tare da biyan kudi ba a bana, bayan Aaron Ramsey, wanda ya koma Turin daga Arsenal bayan da shi ma kwantiraginsa ta kare.


No comments:

Post a Comment