Wednesday, 10 July 2019

Kada ku kara shigowa jihohinmu da shanu a kafa>>Gwamnonin Inyamurai suka gayawa Fulani


Kungiyar gwamnonin yankin Inyamurai sun cimma matsaya da fulani makiyaya da kada su sake zuwar musu da shanu ta kafa watau irin yanda sukan tafiya dasu dinnan suna kiwo zuwa jihohinsu saidai ta kan titi a cikin motoci.

Wannan na cikin sanarwar da Farfesa simon Ortuanya ya fitar ya fitar kamar yanda yake a cikin rahoton jaridar Punch na labarin yau.

Yace akwai fulani makiyaya da suke a yankin kuma ana zaune dasu lafiya, kai wasu ma a nan aka haifesu amma daga baya sai aka fara samun satar mutane dan kudin fansa da kuma rashin jituwa dake kai ga fadace-fadace.

Wannan yasa suka zauna da fulanin dake yankin suka kuma cimma matsayar cewa fulanin ne ke aikata irin wadancan aika-aika amma irin wanda ke shiga yankunan ta kafa ta hanyotin daji da dabbobinsu wanda ma da yawansu ba 'yan Najeriya bane.

Hakan yasa suka amince cewa daga yanzu basu yadda da shiga da dabbobi jihohin nasu ba sai dai ta hanyar kaisu a mota.

Sannan sun bayyana cewa basu da isassun filayen da zasu bayar awa fulanin ruga.

Game da barazanar da wasu (Matasan Arewa) ke yi na korar 'yan kudun daga Arewa, sun bayyana cewa 'yan kudu dake Arewa su kwantar da hankalinsu babu abinda zai samesu dan sun yi magana da gwamnonin Arewa sun basu tabbacin hakan.


No comments:

Post a Comment