Sunday, 7 July 2019

Kalli hotunan Sojan Najeriya 1 daya rage da aka yi yakin Duniya tare dashi

Wannan bawan Allahn me shekaru 104, Adamu Aluko kenan wanda tsohon soja ne da aka yi yakin Duniya na 2 dashi.Shi wannan mutumin shekara daya kawai hadewar Arewa da Kudu da aka yi a shekarar 1914 ta bashi.

Ya hadu da mataimakin shugaban kasa sannan kuma hukumar sojin Najeriya ta karramashi a matsayin daya daga cikin shirin tunawa da 'yan mazan jiya.

Wani abin takaici shine, wannan bawan Allah ya koka akan rashin biyanshi hakkokinshi na Fansho.

Muna fatan Allah ya karawa,Adamu Aluko lafiya.No comments:

Post a Comment