Thursday, 11 July 2019

Kalli hotunan 'yan shi'a da 'yansanda suka gurfanar a Kotu

Labaran yau da jaridar The Nation suka ruwaito sun bayyana cewa wannan hoton na sama na 'yan shi'ane da 'yansandan birnin tarayya, Abuja suka kama dake zanga-zanagar data rikide zuwa hatsaniya dan ganin an saki shugabansu, Sheikh Ibrahim Zakzaky.Labari na cewa ranar Talata 'yan shi'ar suka kutsa kai cikin majalisar tarayya inda suka faffasa gilasan motoci dana ginin majalisar da kuma jiwa wasu 'yansanda ciwo.

Hukumar 'yansandan Abuja ta shaidawa The Nation cewa, ta kama 'yan shi'ar fiye da 40 dan haka zata gurfanar dasu a kotuna 3 saboda yawansu dan a yanke musu hukunci.

No comments:

Post a Comment