Wednesday, 10 July 2019

Kalli hotunan yanda Rahama Sadau ta je Cairo kallon wasan Najeriya da Afrika ta kudu

Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan da suka nuna yanda ta halarci filin wasan da Super Eagles suka yi wasa da kasar Afrika ta kudu a yau dake birnin Cairo na kasar Egypt.Rahamar ta dauki hotunan kamin a fara wasan inda take rike da wani kyalle da aka rubuta Nigeria a jiki.


Hotunan nata sun dauki hankula.

Dazu ne dai mukaga wasu hotunan Rahamar da ta saki wanda ta dauka a Cairo wanda dama hakan ya alamta cewa zata iya zuwa kallon wasan.

Kalli karin hotuna a kasa:
No comments:

Post a Comment