Wednesday, 10 July 2019

Kalli shagon tafi da gidanka da gwamnatin jihar Kebbi ta samar

Domin cimma manufar wannan gwamnatin Karkashin jagorancin Gwamnan jihar, Sanata Atiku Bagudu na bunkasa tattalin arzikin kanan da kuma matsaikaitan 'yankasuwa, maigairma mataimakin gwamnan jihar kebbi Alh. Sama'ila Yombe Dabai ya kirkiro wani shagon tafi -da -gidanka  wanda ya sa wa suna "Keke Bagudu"  don saukaka wa kananan 'yankasuwa gudanar da sana'o'insu a zamanance.Da  manema labarai suka tambaye shi dangane da wannan cigaban, mataimakin gwamnan ya danganta wannan kokarin da burin gwanatin jihar na bunqasa kasuwancin kanana da matsaikaitan 'yan kasuwar jihar.


Mataimakin gwamnan ya kara da cewa"duk lokacin da nake  zagayawa domin shan iska na ga qananan 'yan kasuwa na tura hajarsu a cikin baro, na kan musu kallo  wadanda ka iya taimakawa wajen bunkasa tantalin arziki"

Bugu da kari, mataimakin gwamnan ya kara da cewa Maigirma Gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi amanna cewa idan aka bai wa kananan da matsakaitan 'yankasuwa taimakon da ya cancanta to za su iya yin kafada-da-kafada da sauran 'yankasuwa tsararsu da ke sauran bangarorin kasar nan.

Maigirma mataimakin gwamnan ya karfafa cewa tafarkin da gwamnatin jihar ta dauka na rage fatara da Samar da aikin yi tare da tallafa wa kananan da matsaikatan 'yankasuwa ko shakka babu zai bunkasa tattalin arziki da kuma dorewar zaman lafiya da lumana a jihar.
Rariya.


No comments:

Post a Comment