Tuesday, 9 July 2019

Kalli yanda Ambaliyar ruwa ke kokarin daidaita babban birnin kasar Amurka, har ta taba fadar White House

A jiya, Litinin ne aka samu ruwan sama kamar da bakin kwarya a babban birnin kasar Amurka, Washington DC inda aka samu matsalar ambaliyar ruwa a wasu sassan birnin da suka yi sanadin mutane suka makale akan titi ta yanda dole saidai suka hau saman motocinsu.Hukumar dake kula da yanayi ta kasar tace ta bayyana cewa an yi ruwa me yawa sosai a cikin kankanin lokaci wanda hakan yayi sanadiyyar samun ambaliyar ruwa a birnin, kamar yanda Yahoo news suka ruwaito.

Hukumar ta shawarci mazauna birnin da kada suce zasu yi tafiye-tafiye dan hakan na da matukar hadari, sannan kuma ta shawarci wadanda ke zaune a cikin kwari da su bar guraren dan za'a iya samun ambaliyar ruwa, su nemu tudu su koma dan wannan ambaliyar ruwan ba wadda suka saba gani bace.

Ambaliyar ruwan ta shafi gurin ajiye kayan tarihi da muhimman takardun samun 'yancin kan kasar Amurka da kundin tsarin mulkin kasar da kuma sauran takardun neman 'yanci amma zuwa yanzu hukumomi sun bayyana cewa takardun duk basu tabu ba.

Hakanan ambaliyar ta taba wani bangare na fadar White House, fadar gwamnatin kasar Amurka.

Kalli karin hotuna a kasa:
No comments:

Post a Comment