Wednesday, 31 July 2019

Kalli yanda jama'ar garin Daura suka fito kwasu da kwarkwatarsu dan tarbar Magajin Garin Daura bayan da ya koma gida a karin farko tun bayan da aka yi garkuwa dashi

Jama'ar garin Daura sun fito kwansu da kwarkwatarsu inda sukawa Magajin garin Daura,Alhaji Umar Uba tarba ta musamman bayan dawowa da yayi garin tun bayan da masu garkuwa da mutane suka saceshi.
Bayan da aka cetoshi daga hannun wanda suka yi garkuwa dashi a Kano, an wuce da Magaji babban birnin tarayya, Abuja sannan kuma aka kaishi asibiti a waje inda likitoci suka fuba lafiyarshi.


A yaudai ya koma Garin Daura cikin al'ummarshi.

Ga rahoton da Abubakar Sulaiman ya aiko mana daga garin Daura:
"ALHAMDULILLAH a yaune Allah yayiwa Mai girma Magajin Garin Daura da
wowa gida bayan an kubutar da shi daga hannun masu garguwa da mutane.
Muna godiya ga Allah da malamai da suka ta yamu da addu'ah. Yau garin
Daura ya cika da mutanen gari da baki domin taya al'ummar Daura murna
allah maida kowa gida lafiya by ABUBAKAR SUL AIMAN AT-LIFE 08160816303"


Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment