Wednesday, 31 July 2019

Kalli yanda wani tauraron dan kwallon kafa ya nunawa Duniya yanda yake lalata da wata mata kai tsaye bisa kuskure

Tauraron dan kwallon kasar Kamaru, Clinton N'jie ya bayyanawa Duniya kanshi a shafin Snapchat yayin da yake lalata da wata mata da ba'a san ko wacece ba.Saidai daga baya dan wasan wanda tsohon dan wasan gaba ne na kungiyar Tottenham ya goge hoton bayan da dubban mutanen dake bibiyarshi a shafin suka riga suka kalla.

Daga baya ya bada hakuri inda yace yana murnar komawa sabuwar kungiyarshi ta, Dynamo ta kasar Rasha ce daga kungiyar Olympique Marseille sannan kuma mankas yake da giya.

Yace yana kokarin duba labaraine yaga wane irin labarai kafafen watsa labarai suka buga akan komawar tashi sabuwar kungiyar shine ya danna gurin da ba shi kenan ba amma yana bayar da hakuri,kamar yanda, Orange.fr ta ruwaito.

A shekarar 2015 ne N'jie yaje kungiyar Tottenham inda ya shafe shekaru 2 acan amma bai ci koda kwallo daya ba bayan buga wasa sau 8 kacal, daga baya Tottenham ta sayar dashi ga Marseille ta kasar Faransa.
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment