Friday, 12 July 2019

Kame ko kisa ba zai hanamu zanga-zanga ba>>'Yan Shi'a

Kungiyar 'yan Shi'a dake zanga-zanga dan ganin gwamnati ta saki shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta bayyana cewa kamun da 'yansanda da kuma kisan da suke wa 'yan kungiyar ba zai hanasu ci gaba da zanga-zanga ba har sai an saki shugaban nasu.Memagana da yawun kungiyar, Abdullahi Musa ne ya shaidawa The Nation haka a hirar da ta yi dashi.

Yace, 'yansanda sun kama mana mutane da yawa, wannan kamen ba zai hana mu ci gaba da zanga-zanga ba, kisa ba zai hana mu ci gaba ba kuma ranar litinin me zuwa zamu ci gaba. Zamu tsagaita ranar Juma'a dan mu yi Ibada.

Ya kamata gwamnati ta saki shugabanmu bayan da kotu ta yanke hukunci. Ya kamata gwamnati ta yiwa hukuncin kotu biyayya, basu da wani dalilin tsareshi, rashin lafiyar da yake a hannunsu yanzu tq nuna cewa so suke ya mutu a hannunsu, Injishi.

No comments:

Post a Comment