Saturday, 13 July 2019

Kamfanin mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya shiga maganar sama da fadi da Naira Biliyan 100

Wani kamfanin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo keda hannun jari ciki ya shiga badakalar cin hacin da ake zargin kamfanin dayawa aiki a matsayin sakatare da yayi sama da fadi da Naira biliyan 100.Sunan kamfanin da Osinbajo keda hannun jari a ciki Simmon Coopers kamar yanda me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana a shekarar 2015 lokacin da yake bayyana kadarar mataimakin shugaban kasar.

Ocean Trust Limited ne kamfanin da aka zarga da yin almundahanar kudin wanda shi kuma ya bayyana kamfanin mataimakin shugaban kasar, Simmom Cooper a matsayin sakatarenshi.

Dapo Apara wanda shine daractan kamfanin Alpha Beta ya kaiwa hukumar EFCC korafi da neman su binciki kamfanin na Alpha Beta da yace ya ki biyan gwamnati kudin harajin da suka kai Naira Biliyan 100 kuma kamfanin na Alpha Beta na satar kudinne ta hanyar wani kamfani me suna, Ocean Trust, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Dapo ya gabatar da wancan korafine tun shekarar 2018 inda yayi zargin cewa kamfanin na samun kariya daga wasu jiga-jigan 'yan siyasane a kasarnan dan haka ma yake bugun kirjin cewa babu me iya tabashi.

Dapo yayi kira ga cewa yayi amfani da wannan lokaci da aka samu gwamnati irin ta shugaban kasa, Muhammadu Buhari dake yaki da cin hanci dan ganin an hukunta wannan kamfani.

Saidai da aka tuntubi me magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande yace bazai yi magana ba sai an nuna mai shaidar data nuna cewa kamfanin da ake zargi da almundahanar kudin yayi aiki tare da kamfanin mataimakin shugaban kasar.

Saidai wani na hannun damar mataimakin shugaban kasar ya gayawa Punch a asirce cewa Osinbajo fa bashi da hannun jari a wancan kamfanin dan tun a shekarar 2014 ya bar kamfanin kuma babu dalilin da zai sa EFCC tace ba zata yi bincike akan wannan lamari ba.

Saidai kuma an saka Simmon Coopers a cikin kamfanonin Osinbajo lokacin da ake bayyana kadarorin daya mallaka a shekarar 2015.

Binciken da Punch ta yi ya nuna cewa kamar kamfanin yanzu baya aiki saidai an gano cewa kamfanin na kusa da ofishin tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmad Tinubu.

Saidai shekara daya kenan tun bayan da aka kaiwa EFCC korafi akan wannan kamfani amma har yanzu bata dauki mataki akai ba.

Da aka tuntubi me magana da yawun EFCC, Tony Orilade akan maganar a watan Fabrairun daya gabata, sai yace gaskiya a yanzu EFCC ba zata iya gano inda aka ajiye korafin da mai koken ya aikamata ba amma ya sake aiko da tuni.

A kwanannan kuma da aka sake tuntubarshi me zai ce kan wannan lamari sai yace a bashi lokaci amma har yanzu be yi magana ba.

Tun a lokacin da Tunibu ke gwamnan Legas, wanda a wancan lokacin farfesa Yemi Osinbajone me bashi shawara akan harkokin shari'a, Osinjon yana cikin wanda suka baiwa Tinubun shawarar baiwa kamfanin Alpha Beta kwantirakin karbawa jihar Legas haraji da zummar kamfanin zai rika daukar kaso 10 cikin dari na kudin daya tarawa gwamnatin a matsayin kudin sallamarshi.

Wasu dai na zarin cewa kamfanin na Alpha Beta mallakin Tinubu ne.

No comments:

Post a Comment