Thursday, 11 July 2019

Karanta amsar da Bankin ja'iz ya baiwa wani daya kai musu karar ma'aikacinsu daya bar aiki yaje karbar lambar budurwa

Wani bawan Allah ya kai karar ma'aikacin Ja'iz Bank dake Kano da ya bar aikinshi dan zuwa amsar lambar wayar wata budurwa inda ya rubuta korafin nashi ga bankin ta shafinshi na sada zumuntar Twitter.


Mutumin me suna Najeeb yace yaje reshen bankin dake Zoo road a Kano dan canja lambar wayar da ake aikamai sako da ita, sai yaga wata kyakkyawar budurwa.

Ya rigata gama ab inda zai yi, sai ya tsaya a waje yana jiran ta fito.

Yace daya daga cikin ma'aikatan bankin ya bar aikinshi da mutane suna jiranshi, ya biyo budurwar waje ya karbi lambar wayarta.

Ya kara da cewa da yaga haka sai shi ya fasa aniyarshi. Da ace wannan ma'aikacin naku ya tsaya kan aikinshi da yanzu ina cikin farin ciki, injishi.

Saidai bankin ya bashi amsar cewa, wannan labari naka yana koya darasin cewa ba'a jiran dama ta samu kirkirata ake.No comments:

Post a Comment