Tuesday, 9 July 2019

Karanta martanin Barcelona kan fadan Neymar da PSG

Bayan da ta kacame tsakanin dan wasan PSG dake son komawa tsohuwar kungiyarshi ta Barcelona, Neymar, Barcelonar ta ki cewa uffan ko kuma ta hanzarta sayen dan wasan, kamar yanda ya bukata.Sport English ta ruwaito cewa, da gangan Barcelona taki ma ta ci gaba da neman sayan Neymar din saboda tana jin dadin fadan da yake yi da kungiyar tashi ta PSG.

PSG na neman Yuro miliyan 300 akan Neymar, kudin da Barcelona take fargabar sun yi yawa, dan haka tana tunanin idan fadan Neynar da kungiyar ya ci gaba, dole kungiyar zata nemi sayar dashi da Arha.

Neymar dai yaki komawa Atisaye inda PSG tace be gayamata cewa bazai samu zuwa ba inda har suka yi barazanar daukar mataki akanshi. A martaninshi, Neymar ya bayyana cewa ya gayawa kungiyar bazai samu komawa Atisaye akan lokaci ba.

Barcelona ta yi amfani da kudin da ta sayarwa PSG da Neymar ta siyo Dembele da Coutinho.

A yanzu kuma tana tunanin baiwa PSG wadannan 'yan wasa dan ta kawo Neymar cikin sauki, kamar yanda rahoton ya bayyana.

No comments:

Post a Comment