Friday, 12 July 2019

Kayatattun hotuna daga liyafar cin abincin da shugaba Buhari ya shiryawa 'yan majalisa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan a wadannan hotunan yayin liyafar cin abinci da ya shiryawa shuwagabannin majalisar tarayya da daren jiya,Alhamis a fadarshi dake Abuja.Rahotanni sun bayyana cewa, ba cin abinci kawai aka yi ba, an yi zamanne dan shugaban ya bayyana yanda yake son a amince da sunayen ministocin da zai aikawa majalisar nan gaba ba tare da matsala ba.

Sannan kuma a tattauna yanda za'a shawo kan matsalolin dake cikin kasafin kudi da shugaban ya zargi shuwagabannin majalisar data gabata da yin cushe a ciki.
No comments:

Post a Comment