Monday, 1 July 2019

Ko Jonathan dai haramta auren jinsi yayi: 'yan Najeriya kudu da Arewa sun yi Allah wadai da goyon baya da Amina J. Muhammad ta nuna ga 'yan Luwadi da Madigo

'Yan Najeriya da dama sun yi Allah wadai da kalaman mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya, Amina J. Muhammad da ta yi na nuna goyon baya da baiwa 'ya luwadi da madigo 'yanci kamar kowane mutum.Amina ta yi wannan rubutune a shafinta na dandalin Twitter.

Wani ya rubuta cewa idan hakane sakamkon ilimin matan Arewa to Allah wadai da ilimin nasu ki tunafa zaki yi bayanin abinda kika aikata. Iliminki da wayewarki na iya zama fitina a gareki.
Wani kuwa cewa yayi musulmi daga yankin Arewa ya rika goyon bayan luwadi da madigo, avinda Qur'ani ya haramta? Gaskiya wannan abin da kika yi yasa kin rasa girman da mutane suke ganinki dashi. 

Wani kuwa cewa yayi Duniya ta zo karshe, ga alamu nan a ko'ina. Musulmi na mantawa da addinishi. Allah karka saka mu cikin masu matawa da addinin mu.
Hakanan shima wani yace, Maimakon yin wannan abu da ajiye aikin kikayi da yafi zama Alheri dan kuwa muna da addini da al'ada. Kuma a matsayinki na musulmna be kamata ki yi haka ba. Neman 'yanci ba daya yake da goyon bayan Luwadi da magido ba. Ki sake tunani.
Hakanan shimawani ya bayyana hakan da abin kunya, inda yace kamata yayi ace kina kare addininkine a majalisar dinkin Duniya ba goyon bayan abinda addinin naki ya haramta ba.

Ya kamata dai ki sake tunani.

Kuma koda babu maganar addini ai kina da al'ada.


No comments:

Post a Comment