Friday, 12 July 2019

Kotu ta yi watsi da bukatar hana shugaba Buhari mulki saboda takardun marantarshi sun nuna be cancantaba

Babbar kotun gwamnatin tarayya ta yi watsi da karar da wasu suka shigar suna kalubalantar takardun makarantar shugaban kasa, Muhammadu Buharin inda suka bayyana cewa bai cancanta ya zama shugaban kasa ba.A hukuncin data yanke Yau, Juma'a, kotun ta bayyana cewa ba'a shigar da karar a lokacin da ya kamata ba inda akwai lokutan da aka baiwa damar shigar da kararrakin korafe-korafen kamin zabe kuma lokaci ya wuce a yanzu.

Hakan na nufin kotun ta jaddada hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya.

No comments:

Post a Comment