Friday, 12 July 2019

Kungiyar Izala Ta Yi Kira Ga Shugaban Kasa Buhari Kan A Dawo Da Shirin Ruga Wanda Aka Dakatar

Kiran ya fito daga bakin Shugaban Kungiyar na kasa As-sheikh Imam (Dr). Abdullahi Bala Lau.


Shehun malamin da yake kiran wajen wa'azin kasa da kasa da kungiyar ta gabatar a garin Hadejia Jahar jigawa.

Yace, bamuji dadin yadda Gwamnatin Tarayya tayi magana kan program na ruga, yadda za'a samar da ruga na fulani daga baya tace, ta dakatar saboda maganar wasu mutane "bai kamata ba.

Yakamata gwamnati idan tayi magana ta tsaya akai, ko tace zata duba ta gani saboda wannan program zai temaka waje zaman lafiyar nijeriya.

Masu wannan magana hasada ce, a ransu shiyasa suke sukan wannan program, saboda wata kila gwamnatinsu ta wuce basu irin wannan ba.

Wannan program na ruga wannan kungiya tana kira ga gwamnatin tarayya cewa, adawo da wannan program ayi bayaninsa al'umma su gane fa'idarsa.

Kuma adawo dashi ayishi domin zai amfanar da zaman lafiya.


No comments:

Post a Comment