Thursday, 11 July 2019

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Taraba Ya Bada Katafariyar Gonarsa Kyauta Domin A Gina Makabarta

Kwamishinan 'yan sandan jihar Taraba Sanusi Alkasim ya bada katafariyar gonarsa dake jikin makababartar garinsu wato Sandamu dake Karamar Hukumar Sandamu ta Jihar Katsina kyauta don inganta da fadada makwancin a'lumma bayan rasuwarsu.Tabbas CP Alkasim ya yi matukar kokari wajen bada katafariyar gonarsa kyauta musamman dake cikin gari inda tuni gine-gine sun yawaita a wurin, wanda yin hakan yana da matukar wahala a cikin al'umma duk da irin dumbin ladar da mutum zai kwasa wajen Ubangijinsa. 

 Allah ya saka masa da alheri.

Sannan kuma duk wanda yake da iko ana bukatar sadaka wajen zagaye wannan karin filin makabarta da aka samu. Allah ya ba mu iko. Amin.


No comments:

Post a Comment