Thursday, 11 July 2019

Kwankwaso Ya Samowa Dalibai Gurbin KaratuA Wata Jami'ar Dake Kasar Indiya

A yammacin jiya Laraba 10/7/2019 Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kammala samarwa wasu daga cikin dalibai 370 'ya'yan talakawa gurbin karatu a Jami'ar MEWER UNIVERSITY dake kasar Indiya akan fannoni daban-daban na ilimi, wanda gidauniyar sa ta KWANKWASIYYA DEVELOPMENT FOUNDATION za ta dauki nauyinsu zuwa kasashe daban-daban na duniya.Zuwa yanzu dai Kwankwaso ya ziyarci jami'o'i guda biyu a kasar ta Indiya a cigaba da zagayen nemawa daliban gurbin karatu da yake yi a kasashen duniya a kakar karatu ta bana
(2019/2020 Academic Session).

 Sanata Kwankwaso yana tare da rakiyar jagoran Kwankwasiyya na jihar Kebbi Eng. Abubakar Sadiq Argungu.

Rariya.


No comments:

Post a Comment